Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
FA Cup: Man City ta kai quarter finals bayan cin Bristol City
An wallafa
Manchester City ta je ta ci Bristol City 3-0 a wasan zagaye na biyar a FA Cup ranar Talata ta kuma kai daf da na kusa da na karshe.
Phil Foden ne ya ci biyu da kuma Kevin De Bruyne ya zura na uku a ragar kungiyar da ke buga Championship a fafatawr da suka yi a Ashton Gate.
Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta ci wasa 11 a waje a jere a FA Cup, wadda ke fatan daukar na bana kuma na bakwai jimilla.
Za a ci gaba da wasannin zagaye na biyar ranar Laraba:
- Southampton da Grimsby Town
- Burnley da Fleetwood Town
- Manchester United da West Ham United
- Sheffield United da Tottenham