Real Madrid za ta dauki Bellingham kan Euro miliyan 100

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta amince da yarjejeniyar daukar dan kwallon Borussia Dortmund Jude Bellingham kan Euro miliyan 100.
Dan wasan Ingila mai shekaru 19, ya koma Dortmund daga Birmingham City a watan Yulin 2020, kuma ya kasance dan wasan Ingila da ya mafi haskakawa a gasar cin kofin duniya da aka yi a bara.
Za a gwada lafiyar Bellingham a cikin kwanakin da ke tafe.
Ana saran zai sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru shida.
Dortmund ta tabbatar cewar Real Madrid ta amince za ta sayi dan wasan kan Euro miliyan 103, idan aka hada da karin tsarabe-tsarabe.
Ana kuma cewar cinikin zai kai Euro miliyan 115, idan aka karkare dukkan yarjejeniyar da ta kunshi cinikin dan kwallon.
Tun farko Manchester City da Liverpool suna daga cikin masu son daukar Bellingham, wanda zai zama matashi na uku da aka saya mafi tsada a duniya.
Cikin watan Afirilu, Liverpool ta zanye daga zawarcin Bellinhgam, saboda yawan kudin da Dortmund ta dora buri a kan dan wasan.
Lokacin da Bellingham ya bar Birmingham zuwa Dortmund kan fam miliyan 25 daga gasar Championship, shine mai shekara 17 da aka saya da tsada a lokacin.
Dan wasan ya sa kwazo a gasar Jamus, wanda yake taka rawar gani, ya zama kyaftin din kungiyar a cikin watan Oktoba.
Hakan ya sa ya zama matashin da ya yi kyaftin a kungiyar mai shekara 19.
Bellingham ya buga karawa 42 a bana a Dortmund - ya ci kwallo 14 ya bayar da bakwai aka zura a raga.









