Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ibrahimovic ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a AC Milan
Zlatan Ibrahimovic ya saka hannu kan kwantiragin kaka daya, domin ci gaba da taka leda a AC Milan.
Dan kwallon tawagar Sweden, wanda zai cika shekara 41 da haihuwa cikin watan Oktoba, ya ci kwallo takwas a bara a kakar da Milan ta lashe Serie A.
Likitoci sun yi wa dan wasan tiyata a gwiwar kafa a watan Mayu, wanda ake sa ran zai yi jinyar wata takwas.
Tsohon dan kwallon Manchester United da kuma Paris St-Germain ya koma Milan a 2020, inda ya taimaka mata lashe Serie A, karon farko tun bayan shekara 11.
Ibrahimovic yana kungiyar a lokacin da Milan ta dauki Scudetto, bayan da ya buga mata wasannin aro daga Barcelona da cin kwallo 14 a lik a wasa 29 a kakar 2021.
Daga nan kungiyar ta dauke shi, daga baya ya koma Paris St-Germain a karshen kakar 2011-12.
Wanda ke kan gaba a yawan ci wa Sweden kwallaye mai 62 a raga a wasa 121 ba shi ne kadai ba mai shekara 41 da ke buga tamaula a manyan kungiyoyin Turai ba.
Kyaftin din Real Betis, Joaquin, wanda ya cika sherkara 41 da kwana 21 a watan Yuli, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a kungiyar da ke buga La Liga.