An samar da cibiyar adana nonon uwa ta farko a Najeriya

An samar da cibiyar adana nonon uwa ta farko a Najeriya
An wallafa

A Najeriya kimanin kashi 30 cikin dari na jarirai 'yan kasa da wata shida ana shayar da su nono uwa ne zalla, a cewa Hukumar Lafiya ta Duniya.

An tabbatar cewa shayar da jarirai nono uwa yana da matukar amfani ga lafiyar jarirai kuma a cewar hukumar lafiya ta Birtaniya, ko yaya nono uwa yake yana da amfani.

Dr Chinny Obinwanne ita ce ta kafa cibiyar adana nonon uwa ta farko a Najeriya wadda take a birnin Legas.

Fafutukar da ta dade tana yi wajen ganin ta shayar da 'ya'yanta nononta ita ce ta karfafa mata gwiwar kafa cibiyar.