Arsenal ta kammala daukar Gabriel Jesus

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta kamma daukar dan kwallon tawagar Brazil, Gabriel Jesus, daga Manchester City kan fam miliyan 45, bisa yarjejeniya mai tsawo.
Dan wasan, mai shekara 25, ya zama na hudu da Mikel Arteta ya dauka a bana, bayan Fabio Vieira da Matt Turner da dan wasan Brazil, Marquinhos.
Arteta, wanda ya yi aiki tare da Jesus a lokacin da ya yi mataimin Pep Guardiola a Manchester City na kokarin daukar mai cin kwallaye, bayan da Alexandre Lacazette da Pierre-Emerick Aubameyang suka bar kungiyar.
Jesus, wanda zai sa riga mai lamba tara a Gunners ya bar City, bayan kaka biyar da rabi da ya yi a Etihad.
Ya yi wasa 236 da cin kwallo 95 da lashe Premier League hudu da League Cup uku da FA Cup.
City wadda ta dauki Premier League a kakar da ta wuce ta sayar da Jesus ne, bayan da ta dauko dan kwallon Norway, Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 51.2 a watan Yuni.
Ana kuma sa ran matashin dan wasan tawagar Argentina Julian Alvarez zai fada cikin 'yan kwallon da ke yi wa City wasanni.
Jesus ya bayar da kwallo takwas aka zura a raga a Manchester City a kakar 2021-22, wanda ya yi kan-kan-kan da Kevin de Bruyne a wannan bajintar.











