Donald Trump zai gurfana gaban kotu kan zargin laifukan tsaron Amurka

An wallafa

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya isa Miami, inda zai gurfana a gaban kotu a ranar Talatar nan, kan manyan laifuka da suka danganci rike wasu takardun sirri na tsaro, bayan ya bar mulki.

Zai kuma fuskanci tuhuma kan kokarin hana jami’an tsaro da suka nemi dawo da takardun.

Tun a cikin dare ne tsohon shugaban na Amurka ya sauka a birnin na Miami da ke jihar Florida kafin ya bayyana a kotun, inda zai fuskanci tarin tuhuma kan rike takardun manya-manyan sirrin tsaro na Amurka, ciki har da na makaman nukiliya.

Wannan dai shi ne karo na biyu da zai fuskanci tuhuma ta manyan laifuka.

Wani lauya da ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga kwamitin harkokin shari’a na majalisar wakilan Amurkar a lokacin da ake shirin tsige Trump din karo na biyu, Norman Eisen, ya gaya wa BBC cewa tsohon shugaban zai fuskanci mawuyacin hali a kotun.

Ya ce; ‘’ Ina ganin tuhumar na da karfi sosai. Daga cikin tarin matsalolin Donald Trump, wannan kila za ta kasance laifin shari’a mafi girma. Saboda akwai kwakkwarar sheda da ke nuna cewa ya dauki abin da muke kira bayanan tsaro na kasa, da tsare-tsare na kai harin soji kan wasu kasashe da shirye-shirye na yadda za a iya kawo mana hari da bayanai a kan sirrin nukiliya da abokan gabarmu da abokananmu da kawayenmu. Ya dauki duka wadannan ; babu wani dalili na shari’a da zai sa ya yi haka.''

Mista Trump wanda yake fafutukar neman sake komawa kan mulkin Amurka a shekara mai zuwa, 2024 kamar ko da yaushe a yanzu ma ya musanta aikata wani abu na ba daidai ba, yayin da yake fuskantar tuhumar manyan laifuka ta farko ta gwamnatin tarayya a kan wani tsohon shugaban Amurka.

Trump wanda ya sauka a wajen shakatawarsa na Trump Doral a kusa da birnin na Miami, ya je can ne daga wurin shakatawarsa na wasan golf da ke Bedminster a jihar New Jersey.

An gan shi gum da bakinsa amma kuma da alamun karsashinsa da ya saba lokacin da ya shiga wurin da yamma.

Ya rika daga hannu na karfafa gwiwa da nuna jajircewa ga baki har ma da daukar hoto da wasu daga cikin wadanda ke wurin suna cin abinci da shaye-shaye.

Wasu daga cikinsu magoya bayansa da suka yi takakka takanas daga wasu wurare domin yin zanga-zangar goya masa baya.

Tuni ‘yan sanda a birnin suka ce sun daura damara ta fuskantar wannan zanga-zanga da magoya bayan Trump din za su iya yi, komai girmanta.