Arsenal na son Martinez, Osimhen ya fi son ya tafi Juve

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 25, yana daga cikin zaɓin Manchester City domin maye gurbin ɗanwasan Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (Athletic - subscription required)

Arsenal a shirye take ta biya fam miliyan 128 kan ɗanwasan Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 27. (Fichajes - in Spanish)

Chelsea na shirin biyan Manchester United fam miliyan biyar domin sayen ɗanwasan gaba na Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, (Sun Club - subscription required)

Ɗanwasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 26, ya fi son ya koma Juventus ko kuma gasar Premier idan har ya kammala wa'adinsa a Galatasaray a matsayin ɗanwasan aro. Chelsea da Arsenal da Manchester United duka suna sha'awar ɗanwasan wanda farashinsa ya kai fam miliyan 55. (ESPN).

Ɗanwasan tsakiya na Brentford da Najeriya Frank Onyeka, mai shekara 27, zai koma ƙungiyar idan wa'adinsa ya ƙare a Augsburg inda ya tafi a matsayin aro. (Florian Plettenberg)

Bayern Munich da Ajax na sa ido kan matashin ɗanwasan Manchester City da Ingila Divine Mukasa, mai shekara 17, kodayake City na son tsawaita kwangilar shi. (Fabrizio Romano)

Kocin Chelsea Enzo Maresca na shirin tasara tawagarsa a kaka mai zuwa ba tare da ɗanwasan gaba na Ukraine ba Mykhailo Mudryk, mai shekara 24, da kuma ɗanwasan gaba na Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27. (Sun Club - subscription required)

Arsenal na shirin taya ɗanwasan tsakiya na Real Madrid da Turkiyya Arda Guler, mai shekara 20, kan fam miliyan 25. (Fichajes - in Spanish)