Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern ta yi wasa biyar a jere ba tara da an doke ta ba a Bundesliga
Bayern Munich ta yi wasa na biyar a jere ba tare da rashin nasara ba, bayan da ta doke Heidenheim 4-2 ranar Asabar a Bundesliga.
Jamal Musiala ne ya ci biyu, sai Dayot Upamecano da Leon Goretzka da kowanne ya zura ɗaya a raga.
Ita kuwa Heidenheim ta ci biyu ne ta hannun Honsak da kuma Dorsch.
Bayern ta fara wannan ƙwazon tun bayan da ta doke Bochum 5-0 ranar 27 ga watan Oktoba a babbar gasar tamaula ta Jamus.
Da wannan sakamakon Bayern ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin Bundesliga da tazarar maki shida tsakani da Eintracht Frankfurt wadda ta yi 2-2 da Augsburg.
Kociyan Bayern, Vincent Kompany ya yi karawar ba tare da Harry Kane da Manuel Neuer da Mathys Tel da Serge Gnabry ba, yayin da Musiala ya fara daga benci.
Bayern Munich ta rike wasan da kaso 86 cikin 100 da raba ƙwallo tsakanin ƴan wasanta sau 505, ita kuwa baƙuwa ta yi 51.
Bayern za ta fuskanci Shakhtar Donetsk a Champions League ranar Talata daga nan ta kece raini da Mainz ranar Asabar a Bundesliga.