Palace ta ƙi sallama tayin da Tottenham ta yi wa Guehi

Mark Guehi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Crystal Palace ta yi watsi da tayin da Tottenham ta yi wa mai tsaron bayanta, Marc Guehi kan £70m.

Ɗan wasan tawagar Ingila, wanda Newcastle ta yi sha'awar ɗauka a bana, yana da sauran ƙwantiragin wata 18 a Palace.

Ya buga wasa 23 a bana da cin ƙwallo uku a Premier League, yayin da Palace take mataki na 12 a kan teburi a saman Tottenham da take ta 14.

Ba a sa ran Tottenten za ta kara farashi kan tayin da ta yi wa ɗan wasan mai shekara 24, kafin a rufe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo ranar Litinin.

Palace ta yi watsi da tayi huɗu da Newcastle ta yi wa Guehi, wadda ta so sayen ɗan wasan kan £65m.

An ce Chelsea ta lissafa Guehi cikin masu tsare baya da take son saye, duk da ita ce ta sayar da shi ga Palace kan £18m a 2021.

Ƴan wasa uku ne masu tsare baya da Palace take da su masu koshin lafiya, bayan Trevoh Chalobah da ta dawo da shi wanda ya buga wasannin aro a Chelsea da kuma Chadi Riad.

Tottenham na fama da ƴan wasa da yawa da ke jinya, koda yake ta samu damar ɗaukar aron Kevin Danso daga Lens ranar Lahadi.

Wasu rahotanni na cewar Tottenham na auna yadda za ta ɗauki mai tsaron baya daga Chelsea, Axel Disasi da ɗan wasan AC Milan, Fikayo Tomori.

An tuntuɓi Tottenham ko za ta yi karin bayani.