Fiorentina ta ɗauki tsohon golan Man United David de Gea

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Fiorentina mai buga Serie A ta kammala ɗaukar tsohon mai tsaron ragar Manchester United, David de Gea.

Mai shekara 33 ya zauna bai da ƙungiya a bara, tun bayan da ƙwantiraginsa ya kare a karshen kakar 2022/23

Fiorentina ta sanar cewar za ta gabatar da De Gea gaban magoya baya ranar Litinin 12 ga watan Agusta, amma ba ta fayyace tsawon yarjejeniyar da suka ƙulla ba.

De Gea ya buga wa United wasa 545 a kaka 13 da ya yi, wanda ya lashe Premier League a ƙungiyar a 2012-13.

Ya kuma dauki League Cup biyu da FA Cup da kuma Europa League a lokacin da ya tsare ragar ƙungiyar ta Old Trafford.

Fiorentina, wadda ta kare a mataki na takwas a teburin Serie A a 2023-24, rabon da ta lashe wani babban kofi tun 2001, wadda ta ɗauki Coppa Italia.

An doke ƙungiyar karo biyu a wasan karshe a Uefa Conference League, yanzu kuma tana buga wasannin cike gurbin shiga gasar ta zakarun Turai ta bana.