Man City ta na son ɗaukar Anderson kan Wharton, yayin da Napoli ke harin Kobbie Mainoo

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City sun kamlaa shirin ɗaukar ɗan wasan Nottingham Forest Elliot Anderson mai shekaru 23, kan ɗan wasan gaban Ingila da Crystal Palace Adam Wharton a matsayin siyen ƴan wasan a kakar siyen ƴan wasa ta 2026. (Mail)

Sunderland sun shirya kokawar ɗauko ɗan wasan Lazio da Nwecastle Matteo Guendouzi, mai shekaru 26. (Teamtalk)

Napoli sun shigar da buƙatarsu ga Manchester United kan yiwuwar ɗaukar ɗan wansan Ingila Kobbie Mainoo mai shekaru 20 da ke taka leda a ƙungiyar. (Football Italia)

Atletico Madrid ta shiga cikin jerin masu son ɗaukar Crystal Palace Marc Guehi, mai shekaru 25. (Marca - in Spanish)

Real Madrid sun fasa ɗaukar ɗan wasan Liverpool mai shekari 26 Ibrahima Konate, yayin da kwantaraginsa za ta ƙare a ƙarshen kakar wasannin nan. (Athletic - subscription required)

A shirye Liverpool ta ke wajen ci gaba da riƙe Konate, sai dai ta ce dole sai an sake duba kwantaraginsa, wajen ganin ya tafi dai-dai da tsarin albashinsu. (Sky Sports)

Ɗan wasan Crystal Palace da Fransa Jean-Philippe Mateta, mai sjekaru 28, na so komawa AC Milan da saura ƙungiyoyin ƙwalllon ƙafa da ke Italiya da masu buga Premier League. (Fabrizio Romano)

Manchester City, na son ɗaukar ɗan wasan Newcastle da Ingila Tino Livramento, mai shekaru 23, ya yin da take fuskantar zazzafara takarar ɗaukar sa daga Manchester United da Arsenal. (Caught Offside)

Arsenal na tuntuɓar Juventus don ɗaukar ɗan wasan Kenan Yildiz, mai shekaru 20. (La Repubblica - in Italian)

Ɗan wasan Colombia da Fortaleza CEIF mai shekaru 17 Cristian Orozco, 17, zai koma Ingila don rattaba hannun kan yarjejeniyar kwantaragin komawa Manchester United a kwanaki masu zuwa. (Fabrizio Romano)

Nottingham Forest na sa ido kan mai tsaron ragar Derby County Jacob Widell Zetterstromm sai dai har yanzu dan wasan bai kai ga amincewa da tayin nasu ba. (Sky Sports)