...Daga Bakin Mai Ita tare da Sani Danja

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
...Daga Bakin Mai Ita tare da Sani Danja
An wallafa

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Sani Musa Danja, wanda shahararre ne a Kannywood.

Baya ga fitowa a cikin fina-finan, Danja yana shiryawa da kuma ba da umarni a ƙarƙashin kamfaninsu mai suna 2 Effects. Kazalika, mawaƙi ne a harsunan Hausa da Ingilishi.

An haife shi a unguwar Fagge da ke ƙwaryar birnin Kano, kuma ya yi firamare da sakandarensa a birnin, inda a yanzu yake karatu a buɗaɗɗiyar jami'a wato open university.

"Ni mutum ne mai ra'ayin kawo gyara a cikin al'umma a kodayaushe, shi ya sa na shiga harkar fim," kamar yadda ya shaida wa BBC.