Wane ne Marwan Barghouti, jagoran Falasɗinawa da ake ambatar sunansa a yarjejeniyar tsagaita wuta?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Manar Hafez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Amman
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Ɗan siyasar nan na yankin Falasɗinawa, Marwan Barghouti, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Fatah, wanda yanzu haka ke tsare a wani gidan yari da ke Isra'ila, ya kasance ginshiƙi a tattaunawar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, wadda aka cimma a ranar Alhamis, akwai batun sakin fursunoni Falasɗinawa da kuma ƴan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su.
Wane ne Barghouti, kuma me ya sa batun sakinshi ke haifar da ruɗani?
Marwan Barghouti ya fara shiga harkar siyasa ne lokacin da yake ɗan shekara 15 da haihuwa ƙarƙashin ƙungiyar Fatah, wadda a wancan lokacin ke ƙarƙashin jagoran Falasɗinawa Yasser Arafat.
Barghouti ya shiga gaba-gaba wajen hanƙoron ƙwato wa yankin Falasɗinawa ƴanci da kuma tabbatar da yarjejeniyar kafa ƙasa biyu a yankin.
Ya yi suna a matsayin jagoran Intifada na biyu, kuma ya shafe sama da shekara 20 a gidajen yarin Isra'ila.
Isra'ila ta kama Barghouti a shekarar 2002, lokacin da ta zarge shi da kafa rundunar 'shahidai' ta Al-Aqsa Martyrs Brigade, zargin da ya musanta.
Rundunar Al-Aqsa Matrys Brigade ta ƙaddamar da jerin munanan hare-hare, waɗanda suka hallaka sojojin Isra'ila, da fararen hula da kuma ƴan kama wuri zauna.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A 2004, an yanke wa Barghouti ɗaurin rai-da-rai guda biyar, baya ga ɗaurin shekara 40 kan rawar da ya taka a hare-haren.
Jagoran na Isra'ila ya ƙi amincewa da hurumin kotun ta Isra'ila a lokacin shari'ar tasa, kuma ya yi watsi da zarge-zargen da aka yi masa.
Matarsa Fadwa, wadda lauya ce a yankin Falasɗinawa, ta shaida wa BBC shekarar da ta gabata cewa 'an tuhumi mijinta da waɗannan laifuka ne ba domin shi ne ya aikata su ba da kansa, sai don shi jagora ne", duk da ta ƙara da cewa Barghouti ya musanta zarge-zargen samar da "rundunar Al-Aqsa Matrys Brigade" a lokacin da ake yi masa tambayoyi.
Yanke masa hukunci ya sanya farin jininsa ya kai ko ina a yankin Falasɗinawa - inda mutanen yankin ke ɗaukar sa tamkar Nelson Mandela na yankin - kuma da dama na ganin cewa shi ne ya fi cancanta ya gaji Mahmoud Abbas a matsayin jagoran hukumar mulkin Falasɗinawa (PA).
Amma za a iya samun hakan ne idan Isra'ila ta amince ta sake shi daga gidan yari.
Yiwuwar fitar da shi daga yankin Falasɗinawa

Asalin hoton, Getty Images
Wasu kafofin yaɗa labarai a Isra'ila na cewa akwai yiwuwar Isra'ila za ta saki Barghouti - bisa sharaɗin cewa za a "fitar da shi daga yankin Falasɗinawa".
Anis Al Qassem, masani kan dokokin ƙasa da ƙasa, ya shaida wa sashen Larabci na BBC cewa idan har aka fitar da Barghouti daga yankin Falasɗinawa to babu abin da zai hana shi zama jagoran gwamnatin Falasɗinawa daga ƙasar waje.
An sha samun gwamnatin da ake tafiyar da ita daga ƙasashen ƙetare, musamman a lokacin yaƙin duniya na biyu, kuma dokoki da kuma tsarin mulkin Falasɗinawa bai haramta hakan ba.
Al Qassen ya ce dalilin da zai sa Isra'ila ta yi ƙoƙarin fitar da Barghouti daga yankin Falasɗinawa shi ne "matuƙar farin jininsa a yankin Falasɗinawa, musamman a ɓangaren jagorancin ƙungiyar Fatah."
Cibiyar bincike da tsare-tsare ta Falasɗinawa, wadda ke samun wani ɓangare na kuɗaɗenta daga Tarayyar Turai, ta wallafa sakamakon jin ra'ayin al'umma a ranar 13 ga watan Disamban 2023, wanda ya nuna cewa mutane da dama za su so Marwan Barghouti ya zama jagoran Falasɗinawa.
Sakamakon ya nuna cewa in da za a yi zaɓen shugaban ƙasa a wancan lokaci, tsakanin Barghouti na Fatah, Mahmoud Abbas na Palestinian Authority, da kuma jagoran Hamas (kafin a kashe shi), Isma'il Haniyeh, a matsayin ƴan takara, sakamakon zai nuna cewa Barghouti zai lashe kashi 47% na ƙuri'un, Haniyeh zai samu 43%, yayin da Abbas zai samu 7%.
An yi tunanin cewa Barghouti zai tsaya takarar shugaban yankin Falasɗinawa a watan Yulin 2021, zaɓen da Mahmoud Abbas ya soke bisa hujjar cewa Isra'ila ta ƙi bari mutanen Gabashin Jerusalem su shiga zaɓen.
'Ɗan takarar da aka amince da shi'
Barghouti ya bayyana cewa yana goyon bayan tattaunawar zaman lafiya da kuma maslahar samar da ƙasa biyu, bisa iyakokin da aka zayyana gabanin shekarar 1967.
Ya rubuta wata maƙala da aka wallafa a jaridar Washington Post a shekarar 2002, inda ya ce "Yayin da ni da Fatah, ƙungiyar da nake ciki, muke nuna ƙiyayya ga kai hari kan fararen hula a Isra'ila, maƙwafciyarmu ta nan gaba, ina da haƙƙin kare kaina, na bijire wa mamayen Isra'ila a ƙasata da kuma yin gwagwarmaya domin ƙwatar ƴanci."
Barghouti, wanda ke tsare a gidan yarin Isra'ila tun cikin shekara ta 2002, na iya zama "zaɓin kowa" wanda zai jagorancin gwamnatin mulkin Falsɗinawa, a kan hanyar yankin na samun ƴanci.
Duk da cewa ƴan Isra'ila da yawa ba su son a sake shi kasancewar an same shi da laifin kisa har guda biyar, wasu na ganin cewa sakin shi zai sanya a samu hadin kan Falasɗinawa, lamarin da zai hade ƙungiyoyin da ke adawa da juna wuri ɗaya, wanda hakan zai sanya a samu sauƙin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
An haifi Barghouti ne a shekarar 1958 a ƙauyen Kobar, kusa da birnin Ramallah.
Yana ɗan kimanin shekara 9 ne Isra'ila ta mamaye Gaɓar Yamma da kuma Gabashin Birnin Ƙudus a lokacin yaƙin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967.
Yana da shekara 15 da haihuwa ya faɗa tsundum ciki al'amuran ƙungiyar Fatah ta marigayi Yasser Arafat.
A shekarar 1978 Isra'ila ta kama shi, ta kulle bisa zargin kasancewa ɗan wata ƙungiyar ƴan bindiga ta Falasɗinawa.
Barghouti ya kammala karatun Sakandire inda ya koyi harshen Hebrew a lokacin da yake zaman gidan yari, sannan bayan sakinshi, ya fara karatun digiri a jami'ar Birzeit University.
Ya kwashe kimanin shekara 11 kafin kammala karatunsa, sai dai ya ci gaba da harkokinsa na siyasa, inda har ya zamo jagoran dakarun matasa' na Fatah, wadda ta yi ƙaurin suna a daidai lokacin da manyan ƙungiyar, kamar Arafat da Abbas suke gudun hijira a Lebanon da Tunisia.
Ya tsallake wani yunƙurin kashe shi da Isra'ila ta yi a shekarar 2001, lokacin da aka jefa wa motar masu tsaronsa makami mai linzami.
Barghouti na da ƴa mace guda ɗaya da yara maza uku, kuma yana auren wata lauya kuma mai hanƙoron siyasa, mai suna Fadwa.











