Suarez ya buga wa Uruguay wasan karshe

Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Luis Suarez ya kawo karshen shekara 17 da ya buga wa Uruguay tamaula, inda suka tashi 1-1 da Paraguay a wasan neman shiga gasar kofin duniya.

Ranar Litinin Suarez ya sanar cewar zai yi ritaya da zarar an tashi karawa da Paraguay a wasan neman shiga kofin duniya daga Kudancin Amurka.

Shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar ƙwallaye a tarihi mai 69 a raga a karawa 143, tun bayan da ya fara yi mata tamaula a wasa da Colombia a Fabrairun 2007.

Suarez da iyalansa da sauran ƴan wasa sun taru a cikin fili kafin take leda, inda aka yi bikin ban kwana ga ɗan wasan, Lionel Messi ya aike da sakon fatan alheri a filin.

Uruguay ta mamaye wasan da kaso 65 cikin 100, amma ta kasa ratsa bayan Paraguay a wasan da aka yi laifi 24 da raba katin gargadi shida har da wanda aka bai wa Suarez.

Uruguay ta buga fafatawar ba tare da manyan ƴan wasanta biyar ba, waɗanda aka dakatar ciki har da ɗan wasan Liverpool, Darwin Nunez da na Tottenham, Rodrigo Bentancur, bayan hatsaniya lokacin Copa America da Colombia a watan Yuli.

Da wannan sakamakon Uruguay tana ta biyu a teburi da maki huɗu tsakani da Argentina ta ɗaya a wasannin nemna shiga gasar kofin duniya daga Kudancin Amurka.

Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images