Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Brentford ta amince wa Al-Ahli ta Saudiyya ta sayi ɗan wasanta Toney
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football news reporter
- Marubuci, Nizaar Kinsella
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport football news reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Brentford ta amince da tayin fan miliyan 40 kan ɗan wasan gabanta Ivan Toney daga ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya.
Majiyoyi da ke kusa da ɗan wasan na Ingila sun ce sun yi amanna cinikin zai faɗa.
Toney mai shekara 28 bai buga wa Brentford wasa ba a wannan kakar tukunna kuma kociya Thomas Frank ya cire shi daga tawagar da za ta buga masa wasa da Southampton ranar Asabar.
Ƙungiyar ta ƙi amincewa da tayin fan miliyan 35 daga Al-Ahli tun da farko kafin fara sabuwar kaka, sannan kuma an yi ta alaƙnta shi da Chelsea a 'yan makonnin nan.
Shi ma ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen, ana alaƙanta shi da koma Al-Ahli.
Kasuwar saye da musayar 'yan wasan Saudiyya ba za ta rufe ba har sai ranar 2 ga watan Satumba, saboda haka ba lallai ne sai an kammala cinikin Toney ba a ranar Juma'a.
Toney na cikin manyan 'yan wasan Ingila da za su koma Saudiyya, kamar yadda Jordan Henderson ya koma Al-Ettifaq daga Liverpool a watan Yulin 2023 - sai dai daga baya ya koma Ajax.