Ban taɓa haɗuwa da mutum kamar Unai Emery ba - McGinn

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kyaftin John McGinn ya ce bai taɓa haɗuwa da wani mutum ba kamar Unai Emery wanda tuni ya samu gurbi cikin tarihin gwarazan ƙungiyar Aston Villa.

Ƙoƙarin Villa da ta fara a wannan kakar na ci gaba bayan nasarar 2-0 da ta samu kan Bologna tare da zama ta ɗaya a jadawalin Champions Lig.

Emery wanda zai cika shekara biyu da zuwa Villa Park a ranar Alhamis, ya taimaka wa ƙungiyar shiga jerin huɗun farko a Premier a wannan kakar, maki huɗu ne tsakaninta da Liverpool da ke ta ɗaya.

Mai shekara 52 har yanzu bai ci kofi ba a ƙungiyar amma kyaftin McGinn ya yi amannar ya samu wurin zama a ƙungiyar.

"Ko me zai faru sai dai in shi ya ce zai bari - kuma ba ma fatan hakan - da sannu zai zama cikin manyan kocin ƙungiyar nan da suka kafa tarihi," in McGinn.

"Kai ne za ka bai wa shugabanka abin da kake so. Shi ne sugabanmu kuma yana yin abin da yake so. Babu wanda zai tambayi me yake yi wa ƙungiyar, ko me yake yi a yanzu shi ake kira aiki tukuru.

"Ni dai ban taɓa haɗuwa da wani mutum kamarsa ba," kamar yadda ɗan shekara 30 ɗin ya bayyana.