Ku San Malamanku tare da Gwani Sani Usman Tilo

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Ku San Malamanku tare da Gwani Sani Usman Tilo
An wallafa

Sani Usman Tilo gwanin Alƙur'ani ne da aka haifa a unguwar Fagge da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.

Ya yi karatu a wurin malamai da dama kamar Malam Dan Ringim wanda ɗan'uwan mahaifinsa ne. Ya yi haddar Ƙur'ani a hannun Malam Murtala a Kano.

Ya koyi ilimin Tajawidin Ƙur'ani a hannun Gwani Yahuza Dan Zarga a birnin na Kano.

Ya rubuta Ƙur'ani karon farko a 1994 kuma yana cikin limaman masallacin Juma'a na Ibadul-Rahman da ke unguwar Tudun Yola.