Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Majalisar Dinkin Duniya ta gargaɗi Isra’ila kan ƙaddamar da hari a Rafah
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin kan shirin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a cikin birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza.
Shugaban hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, Martins Griffiths ya ce lamarin zai kai ga aikata gagarumar kisan fararen hula domin kuwa akwai Falasɗinawa fiye da miliyan ɗaya da ke neman mafaka a Rafah.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Falasɗinawa fiye da miliyan ɗaya da ke cunkushe a Rafah basu da wani wajen tserewa idan aka fara lugude a yankin.
Mai magana da yawun sakatare janar na Majalisar, ya shaidawa BBC cewa Majalisar Dinkin Duniya ba zata shiga cikin tilastawa mutane fita daga Rafah ba, kuma babu wata alama da ke nuna cewa Isra’ila tana da shirin kwashe fararen hula.
Ya ce: "Ko a yanayin zaman lafiya wannan aiki ne da ke buƙatar a tsara shi da kyau, kuma na tsawon lokaci kafin aiwatarwa. To yaya ake tunanin gudanar da irin wannan aiki a lokacin yaƙi da rikici....a yanayin da babu tsaro, ga kuma gine-gine kamar za su rushe.'’
An dai kammala zaman ranar farko don tattauna batun tsagaita wuta a Gaza, kuma da alama taron na birnin Alkhahira na ƙasar Masar bai cimma wata matsaya ba.