Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta yi canjaras biyu a jere da fara Premier League ta bana
Liverpool da Crystal Palace sun rabi maki a tsakaninsu, bayan da suka tashi 1-1 a Anfield a wasan mako na biyu a gasar Premier League.
Palace ce ta fara cin kwallo a minti na 32 ta hannun Wilfried Zaha, ya zama dan wasan Palace da ya ci Liverpool karo biyu a Anfield na farko a Mayun 2015.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka bai wa sabon dan kwallon da Liverpool ta dauka a bana Darwin Nunez jan kati.
Ya zama na biyu wanda ya karbi jan kati a wasan farko Premier League a Anfield, bayan Joe Cole a fafatawa da Arsenal a 2010 kuma a ranar 15 ga watan Agusta.
Daga baya Liverpool ta farke kwallon ta hannun Luis Diaz.
Karo shida kenan da ake fara cin Liverpool kwallo daga baya ta farke a Premier League, wadda ta taba yin haka tsakanin Afirilu zuwa Agustan 1997.
Sai dai a karawa biyar baya ta ci wasa uku da canjaras biyu, kenan ba ta taba yin rashin nasara ba.
Liverpool ta fara da yin 2-2 a makon jiya da Fulham a Craven Cottage, yayin da Palace ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Arsenal a Selhurt Park.
Wasan na Liverpool da Crystal Palace an yi shi a ranar da gasar Premier League ta cika shekara 30 da farawa, wato ranar 15 ga watan Agustan 1992.
Sai dai kuma a ranar Liverpool ba ta yi wasa ba, amma Palace ta tashi 3-3 da Blackburn a Selhurst Park.