Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin kun san muhimmancin tsayar da lokacin barci ga lafiyarku?
Bambance-bambancen da ake samu dabi’ar barci tsakanin ranakun aiki da na hutu ka iya haifar da sauye-sauye na rashin kiwon lafiya ga kwayoyin bacteria da ke cikin ‘yayan hanjinmu, a cewar wani bincike.
Hakan ka iya kasancewa sakamakon mutane masu matsalar jinkiri wajen yin barci da ake kira 'social jetlag', da kuma marasa bin tsarin cin abinci mai kyau, a cewar masu binciken na Birtaniya.
An bayyana cewa barcin ake matukar katsewa, musamman a lokacin yanayin aiki na canji, na yin mummunan tasiri wa lafiyar jiki.
Daidaita lokutan barci da kuma tashi yadda ya kamata, tare da cin abinci mai gina jiki ka iya taimakawa wajen rage hatsarin kamuwa da rashin lafiya.
Binciken da masana kimiyya suka gudanar a kan manya kusan 1,000 a kwalejin Kings College London, ya gano cewa ko da bambancin minti 90 a tsakiyar barcin dare, ka iya yin tasiri a kan kwayar bacteriyar da ake samu a cikin hanji ko cikin dan adam.
Kasancewar nau’ika daban-daban na ƙwayar bacteria a cikinka yana da matukar muhimmanci.
Wasu sun fi wasu amfani, amma samun wadanda suka dace shi ne muhimmi wajen samun kariya daga cututtuka da dama.
"Masu fama da matsalar jinkiri wajen yin barci ka iya karfafa wa ƙwayoyin halittar bacteria marasa amfani wa lafiyarsu,’’ a cewar Dakta Kate Bermingham, marubuciyar binciken, sannan babbar jamai’a a fannin kimiyyar abinci a kamfanin kimiyyar abinci na Zoe.
Kwanciya barci da tashi daga barci a lokuta daban-daban a cikin mako, idan aka kwatanta da ƙarshen mako, na shafar kashi 40 bisa dari na yawan al’ummar Birtaniya, a cewar binciken, sannan an fi samu a tsakanin matasa, sannan yakan ragu a yayin da muke ƙara shekaru.
Waɗanda aka gudanar da binciken a kansu a mujallar abinci ta 'European Journal of Nutrition', an yi gwaje-gwaje a kan yanayin barci da kuma jininsu, kana aka karbi samfurin bayan tattara bayanan duk abubuwan da suka ci a cikin wata takardar tambayoyi kan abinci.
Akwai yiwuwar kashi 16 bisa dari na wadanda ke fama da matsalar samun jinkirin yin barci su ci nau’ikan abincin da aka sarrafa da dankalin Turawa da suka kunshi kayau-kayau, da soyayyen dankalin, da abubuwan sha masu zaki, da karancin ‘yayan itatuwa da nau’ikan gyada.
Binciken da aka gudanar a baya ya nuna mutanen da ke da matsalar jinkiri wajen yin barcin sun ci abinci mai dusa kadan, idan aka kwatanta da wadanda ke da lokutan barci masu dorewa.
Sauran binciken sun gano masu matsalar jinkiri wajen yin barcin na da dangantakata da kara kiba, da kamuwa da cututtuka da kuma tsananin kasala.
"Rashin ingantaccen barci na tasiri a kan zabi daban-daban – kana mutane kan ji kwadayi cin abinci mai zaki,’’ a cewar Dakta Bermingham.
Tasirin rashin tsarin cin abinci mai kyau ga lafiyar bacci
Masu bincike sun gano cewa uku cikin nau’ikan kwayoyin bacteria shida da suka fi yawa a cikin ‘yayan hanjin mutanen da ke fama da jinkirin barcin ana danganta su ne da rashin tsarin cin abinci mai kyau.
Dangantaka tsakanin barci, da tsarin cin abinci, da kwayar bacteria ta cikin hanji na da matukar sarkakiya, sannan har yanzu akwai abubuwan da dama da suka kamata a gano, a cewar tawagar masu binciken.
Amma kafin nan, shawararsu ita ce a rika cigaba da dorewa da komai, muddin za a iya, a cikin makon.
"Cigaba da tsarin yin barci yadda ya kamata, idan muka kwanta barci, sannan muka tashi daga barci a kowace rana, dabi’ar rayuwa ce da za mu iya sabawa da ita, da za ta iya yin tasiri wa lafiyarka ta hanyar kwayoyin bacteria na cikin ‘ya'yan hanjinka," a cewar Dakta Sarah Berry, daga kwalejin King's College ta birnin London.
Menene tsarin cin abinci mai kyau?
Shafin yanar gizo na hukumar NHS ya amince da a gwada yin wannan:
- Cin nau’ikan ‘yayan itatuwa da ganyaye akalla biyar a ko wace rana
- Tsara nau’ikan abincinka kamar su dankalin turawa, da burodi, da shinkafa ko kuma taliya
- A rika amfani da madarar shanu, amma mai karancin maiko ko sukari idan da hali
- Cin nau'ikan abinci masu gina jiki kamar su wake da kifi da kwai da nama da sauransu
- Takaita cin abinci da suke da kitse mai yawa a cikinsu, da daskararren mai.
- Yawaita shan ruwa a kowacce rana (Aƙalla kofi sida a kowace rana)