Jurgen Klopp ya yi sanadin korar koci shida a Ingila

An wallafa

Jurgen Klopp ya zama kociyan Liverpool a 2015, wanda ya maye gurbin Brenden Rodgers.

Klopp ya ja ragamar Liverpool zuwa wasan karshe a Champions League a 2018, sai kungiyar ta Anfield ta lashe kofin Zakarun Turai a 2019 na farko a wajensa na shida a Liverpool

Liverpool ta kare a mataki na biyu a kakar 2018/19 a gasar Premier League da hada maki 97 - karo na uku da aka hada maki mai yawa a tarihin babbar gasar tamaula ta Ingila.

A kakar 2019/20 Klopp ya ci Uefa Super Cup da kofin Fifa Club World Cup na farko da Liverpool ta dauka, sannan ya ci Premier League, bayan shekara 30 rabon da kungiyar ta lashe kofin.

Kwazon kociyan ya sa ya lashe kyautar gwarzon koci a duniya a 2019 da kuma 2020.

Kakar 2021/22 Klopp ya ja ragamar Liverpool ta kai wasan karshe a Champions League, wadda ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid a Faransa da ci 1-0.

Sai dai Liverpool ta yi ta biyu a teburin Premier League, biye da Manchester City wadda ta lashe kofin da tazarar maki daya kwal.

Kungiyar ta Anfield ta lashe FA Cup da Caraboa duk a kan Chelsea a wasannin karshe da suka fafata.

Klopp ya ja ragamar Liverpool a kakar 2022/23 da lashe Community Shield, bayan doke Manchester City 3-1.

Sai dai Liverpool ta fara da tashi 2-2 da Fulham a gasar Premier, sannan ta yi 1-1 da Crystal Palace a Anfield da rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester United a Old Trafford.

To sai dai Liverpool ta huce haushinta a kan Bournemouth da ci 9-0 a wasan mako na hudu a Anfield ranar Asabar.

Wannan cin ya sa Bournemouth ta koci Scott Parker daga aikin kociyan Bournemouth.

Hakan ya sa shi ne mai horar da tamaula na shida a Ingila da Klopp ya yi sanadin rasa aiki, bayan da Liverpool ta shi kungiyarsa.

Mohammed Abdu ya hada mana rahoto

Swansea City ta sallami Francesco Guidolin

Francesco Guidolin dan kasar Italiya ya ja ragamar Swansea City wasa da Liverpool ranar 1 ga watan Oktoban 2016, inda Liverpool ta yi nasara da ci 2-1.

Kwana biyu tsakani Swansea City ta sanar da korar Guidolin daga aiki a ranar da yake bikin murnan cikarsa shekara 61 da haihuwa.

West Ham ta kori Slaven Bilic

Ranar 4 ga watan Nuwambar 2017, Liverpool ta je ta doke Wst Ham United 4-1 karkashin jagorancin Slaven Bilic.

Kwana biyu tsakani West Ham ta sanar da sallamar Bilic daga aikin jan ragamar kungiyar.

Fulham ta raba gari da 4. Slavisa Jokanovic

Slavisa Jokanovic ya shiga jerin mai horar da tamaula da aka kore shi bayan karawa da Liverpool karkashin Jurgen Klopp.

Ranar 11 ga watan Nuwambar 2018, Liverpool ta doke Fulham 2-0 - kwana uku tsakani sai aka ji sanarwar an kori Jokanovic.

Manchester United ta raba gari da Jose Mourinho

Ranar 18 ga watan Disamba, Manchester United ta sallami Jose Mourinho daga aiki.

Hakan ya biyo bayan da Liverpool ta ci United 3-1 ranar 16 ga watan Disambar 2018.

Everton ta kori Marco Silva

Marco Silva wanda ke jan ragamar Fulham a yanzu haka a gasar Premier League ta bana, ya taba rasa aiki a Everton, bayan da Klopp ya yi nasara a kansa.

Ranar 4 ga watan Disambar 2019, Liverpool ta casa Everton 5-1 a wasan hamayya.

Washe gari sai aka ji cewar Everton ta sallami kociyan.

Bournemouth ta kori Scott Parker

 

Bournemouth ta kori, Scott Parker, bayan da kungiyar ta sha kashi a gidan Liverpool da ci 9-0 ranar Asabar, bayan wasa hudu da ya ja ragama a Premier League.

Shi ne kocin farko a Premier League bayan shekara 18 da aka sallama cikin Agusta tun bayan Bobby Robson a Newcastle a 2004.

Shi ne na 11 da aka kora bayan wasa hudu da fara kakar tamaula, na karshe-karshe da aka sallama shi ne Javi Gracia a Watford a 2019.

Ranar Talata aka samu sanarwar korar Parker, bayan kwana uku da Liverpool ta caskara Bournemouth.