Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da wa za a hada Real Madrid a Champions League kwata fainals?
Real Madrid za ta san wadda za ta fuskanta a zagayen daf da na kusa da na karshe a Champions League na bana.
Za a raba jaddawalin kwata fainals a gasar ta zakarun Turai ranar Juma'a a 15 ga watan Maris a birnin Nyon a Switzerland.
Watakila Real Madrid ta fuskanci PSG ko Bayern Munich ko Manchester City ko Barcelona ko Arsenal ko Borussia Dortmund ko kuma Atlético Madrid.
Real Madrid mai Champions League 14 ta kawo wannan matakin ne a bana, bayan da ta ja ragamar rukunin na uku da maki 18.
Ranar 13 ga watan Fabrairu Real Madrid ta je ta ci RB Leipzig 1-0 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Jamus.
A wasa na biyu kuwa a Sifaniya, Real da Leipzig sun tashi 1-1 ranar 6 ga watan Maris a Santiago Bernabeu - hakan ya sa ta kai zagayen gaba da cin 2-1 gida da waje.
Jadawalin kwata fainals zai fayyace kungiyar da za ta karbi bakunci da wadda za ta kai ziyara da za a fara karawa ranar 9 ko 10 ga watan Afrilu.
Za kuma a buga karawa ta biyu a zagayen daf da na kusa da na karshe ranar 16 ko 17 ga watan Afirilun.
A kuma ranar Juma'a ake sa ran za a yi jadawalin har da zagayen daf da karshe da za a fara fafatawa daga ranar 30 ga watan Afirilu, sannan a yi wasa na biyu ranar 7 ko 8 ga watan Mayu.
Filin wasa na Wembley ne zai karbi bakuncin wasan karshe a Champions League ranar 1 ga watan Yuni.
Manchester City ce mai rike da kofin bara.