Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa Scones

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa Scones
An wallafa

Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa masu girki damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyo, za ku kalli gwanin girkinmu na yau, da ke nuna mana yadda ake sarrafa scone, don masu azumi.

Bashir Ibrahim Naiya wanda ke zaune a jihar Merrilands ta Amurka ya nuna mana yadda ake haɗa wannan abinci mai daɗi.

Girki ne da mai azumi, ba zai so ya wuce shi ba, idan an sha ruwa!