Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ta ɗauki nauyin karatun 'ya'yanta huɗu har jami'a da sana'ar takalmi
Hausawa kan ce babu maraya sai raggo!
Malama Rabi Idris ta kasance mace ce wadda mijinya ya rasu ya bar ta da yara huɗu a Katsina da ke arewacin Najeriya.
A mafi yawan lokuta matan da mijinsu ya rasu kan shiga wani mawuyacin hali saboda rashin wanda zai dauki nauyinsu da na yaran da aka barsu tare.
Sai dai malama Rabi ba ta yarda ta shiga irin halin da wasu ke shiga ba na jiran wani ya taimake su.
Ta rungumi sana’ar hadawa da sayar da talkalmi, wadda da ita ce ta samu damar daukar nauyin karatun yaranta har matakin jami’a tare kuma da yi ma uku daga cikinsu aure.
Kalli cikakken bidiyon domin jin bayani daga bakinta.