Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jamus ta kira Mario Gotze bayan shekara biyar
Jamus ta kira dan wasan tsakiyarta Mario Gotze cikin tawagar da za ta buga mata Kofin Duniya bayan nusau da ya yi na shekara biyar.
Dan wasan Eintracht Frankfurt Goetze mai shekara 30, shi ne ya jefa kwallon da ta bai wa Jamus nasara a wasan karshe na gasar a 2014.
Rabon da dan wasan ya bugawa Jamus wasa tun wasan sada zumunta da ta yi da Faransa a watan Nuwambar 2017.
Abokan wasansa a Bayern Munich Manuel Neuer da Thomas Muller za su buga gasar karo na hudu a tarihi.
Dan wasan gaba na , Borussia Dortmund Youssoufa Moukoko shekara 17 shi ma na ya samu gayyata.
Jamus da ke rukunin E za ta fara wasanta na gasar Kofin Duniya da Japan a ranar 23 ga watan Nuwamba kafin ta fafata da Spain da kuma Costa Rica.
Tawagar Jamus Masu tsaron raga: Manuel Neuer (Bayern Munich), Marc-Andre ter Stegen (Barcelona), Kevin Trapp (Eintracht Frankfurt)
'Yan wasan baya: Armel Bella-Kotchap (Southampton), Matthias Ginter (SC Freiburg), Christian Gunter (SC Freiburg), Thilo Kehrer (West Ham), Lukas Klostermann (RB Leipzig), David Raum (RB Leipzig), Antonio Rudiger (Real Madrid), Nico Schlotterbeck (Borussia Dortmund), Niklas Sule (Borussia Dortmund)
'Yan wasan tsakiya: Julian Brandt (Borussia Dortmund), Leon Goretzka (Bayern Munich), Ilkay Gundogan (Manchester City), Jonas Hofmann (RB Leipzig), Joshua Kimmich (Bayern Munich), Jamal Musiala (Bayern Munich)
'Yan wasan gaba: Karim Adeyemi (Borussia Dortmund), Niclas Fullkrug (Werder Bremen), Serge Gnabry (Bayern Munich), Mario Gotze (Eintracht Frankfurt), Kai Havertz (Chelsea), Youssoufa Moukoko (Borussia Dortmund), Thomas Muller (Bayern Munich), Leroy Sane (Bayern Munich)