Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Turkiyya: Mutanen da suka mutu a wurin haƙar kwal sun kai 40
Mutanen da suka mutu sakamakon maƙalewa a ƙarƙashin ƙasa a Turkiyya sun kai 40, a cewar ma'aikatar cikin gida.
Kazalika wasu gwammai sun jikkata bayan da aka samu wata fashewa a wajen haƙo gawayin kwal a arewacin lardin Bartin da ke Turkiyya.
Tun farko Ministan Harkokin Cikin Gida Suleyman Soylu ya ce an ceto mutum 58 sannan wasu kusan 20 na maƙale a cikin ramin.
Rahotanni sun ce kusan mutum 110 ne ke aiki a wurin haƙar ma'adinan a lokacin da aka samu fashewar.
Kusan rabin mutanen suna cikin rami mai zurfin sama da mita 300.
Ministan kiwon lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya bayyana cewa ana ci gaba da bai wa mutanen da aka ceto kulawa.
Babu tabbas kan abin da ya jawo fashewar amma dai tuni hukumomi suka soma bincike.
Tun cikin dare ma'aikatan agaji ke ci gaba da tona rami domin nemo waɗanda suke da rai.
Wani bidiyo ya nuna yadda masu haƙar ma'adinan da aka tono su sun yi baƙi inda masu ceto ke rakiyar su a Gabar Tekun Black Sea.gett
Haka kuma a bidiyon an ga ƴan uwa da abokan arziki na waɗanda lamarin ya shafa a wurin da lamarin ya faru inda suka ƙagara su ji labarin ƴan uwansu.
Babu tabbaci kan ko me ya jawo fashewar amma dai tuni hukumomi suka soma bincike a ƙasar.
Haka shi ma ministan makamashi na Turkiyya ya bayyana cewa akwai bincike na wucin gadi da ke nuna cewa wani sinadarin da ke cikin kwal ɗin ne ya haddasa fashewar.
Ana sa ran Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai ziyarci wurin da lamarin ya faru a ranar Asabar.
Magajin garin Amasara Recai Cakir ya bayyana cewa akasarin waɗanda suka tsira sun samu munanan raunuka.