Ku San Malamanku tare da Sheikh Nasir Adam - Limami a jami'ar YUMSUK

Bayanan bidiyo,
Ku San Malamanku tare da Sheikh Nasir Adam - Limami a jami'ar YUMSUK
An wallafa

An haifi Sheikh Nasir Shuaib Adam a unguwar 'Yar Kwaɗi cikin birnin Kano. Ya ce ya fara karatun Al-ƙur'ani ne a gaban mahaifinsa.

Ya yi haddar Ƙur'aninsa ta farko a cikin ƙaramar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a 1998.

Bayan nan ne ya shiga makarantar sakandiren Abdullahi Bayero College of Qur'anic Studies.

Ya yi dgirinsa ta farko a fannin Larabci a Jmai'ar Bayero Kano, kafin ya tafi ƙasar Malaysia, inda nan ma ya ci gaba da karatun digiri na biyu a fannin Larabci.

Sheikh Nasir Shuaib Adam ya fara aikin koyarwa bayan ya koma gida Najeriya, a jami'ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK).