Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tuchel bai ji da dadi ba a gidan Leeds a wasansa na 60 a Premier League
Chelsea ta sha kashi da ci 3-0 a gidan Leeds United a wasan mako na uku a gasar Premier League da suka fafata a Elland Road ranar Lahadi.
Chelsea wadda ta sayo 'yan wasa a bana kan fam miliyan 170, an fara zura mata kwallo a minti na 33 ta hannun Brenden Aaronson, sai kuma Rodrigo ya ci na biyu daf da za a yi hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Leeds ta kara kwallo na uku ta hannun Jack Harrison.
Kwallon da Rodrigo ya ci ya zama karo na uku a jere a wasa uku da fara kakar bana yana zura kwallo a raga ya zama na hudu mai wannan bajintar a Leeds.
Wadanda suka yi wannan kwazon a kungiyar sun hada da Arthur Hydes a kakar 1933/34, Mick Jones a 1968/69 da kuma Partrick Bamford a 2020/21.
Wannan shi ne wasa na 60 da Thomas Tuchel ya ja ragamar Chelsea a gasar Premier League ya sha kashi a karawa ta 10 kenan.
Tuchel din ya ci wasa 33 da canjaras 17 da cin kwallo 104 aka zura 51 a ragar Chelsea tun bayan da ya fara jan ragamar kungiyar a Janairun 2021.
Wannan shi ne karon farko da Leeds United ta yi nasara a kan Chelsea a Elland Road, tun bayan cikin watan Disambar 2002, inda Leeds ta ci 2-0 a lokacin.
An bai wa Kalidou Koulibaly jan kati
Chelsea ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Koulibaly jan kati saura minti shida a tashi daga karawar.
Tun daga fara kakar 2017/18 an bai wa Kalidou Koulibaly jan kati shida a gasar Serie A da kuma Premier League, shi ne kan gaba a rashin da'a a manyan gasar Turai biyar.
Chelsea wadda ta ci Everton 1-0 a wasan farko da tashi 2-2 a gida da Tottenham a makon jiya, za ta karbi bakuncin Leicester City ranar 27 ga watan Agusta a wasan mako na hudu a gasar Premier.
Ita kuwa Leeds United za ta ziyarci Barnsley ranar 24 ga watan Agusta a wasan League Cup da ake kira Caraboa.