Kante zai yi jinyar mako hudu

An wallafa

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce "babban dan wasansa" N'Glo Kante zai yi jinyar a kalla mako hudu sakamakon ciwon da ya ji a cinyarsa.

Dan wasan mai shekara 31 ya samu raunin ne a wasan da Chelsea ta tashi 2-2 da Tottenham, abin da ya sa bai buga wasan da ta yi rashin nasara ba kenan a makon jiya a hannun Leeds.

"Yana yi wa kungiyarmu kokarin da babu wani dan wasa a duniya da yake yi wa kungiyarsa," in ji Tuchel.

"Dan wasanka ya ji ciwo, abu ne mara dadi, amma dole ka nemi mafita. Saboda yana da tasiri.

"Da wuya ka iya maye gurbinsa. Shi dan wasa ne na daban. Mun ta fatan kafa tawagarmu a kansa lokutan da muke buga wasannin share fage."

Duk da dan saukin da ya fara samu game da ciwon gwiwarsa, Dan wasan Croatia Mateo Kovacic, wanda har yanzu bai buga wa Chelsea wasa ba, ba zai buga mata wasan ranar Asabar ba da za ta buga da Leicester ba.

Ana sa ran kocin Chelsea ya zauna a bayan fage a ranar wasan, biyo bayan rikicin da suka yi da kocin Tottenham Antonio Conte.

Dan wasan da ta saya a wannan kakar Kalidou Koulibaly shi ma ba zai buga wasan ba, sakamakon jan katin da aka ba shi a wasan da suka buga da Leeds United.