Tottenham Hotspur ta sayi dan wasan Brazil Richarlison daga Everton

An wallafa

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta sayi dan wasan gaban Brazil Richarlison daga Everton a wata jarjejeniya da aka yi amanna ta kai £60m.

Dan wasan mai shekara 25 ya zura kwallaye 10 sannan ya taimaka aka zura kwallaye biyar lamarin da ya kare Everton daga faduawa daga gasar Firimiya a kakar da ta gabata.

Jimilla, ya zura kwallaye 43 a wasannin lig-lig 135 da ya fafata a kungiyar tun da ta saye shi daga Watford a watan Yulin 2018.

The Hornets sun sayi Richarlison a kan £11.5m daga kungiyar kwallon kafar Fluminense ta kasar Brazil a 2017.

Richarlison ne dan kwallon da ya fi zura kwallo a fafatawar da Everton ta yi a dukkan gasa.

Ya soma murza leda a manyan gasa na duniya a watan Satumbba na 2018 yayin da ya buga wa Brazil kwallo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a wasan da suka doke Amurka da ci 2-0 kuma tun daga wancan lokacin ya buga tamaula a wannan mataki sau 36, inda ya ci kwallaye 14.

A 2019, an sanya shi a tawagar 'yan kwallo 23 da suka fafata a gasar Copa America kuma zura kwallo a wasan karshe lamarin da ya sa Brazil ta lashe Kofin a karon farko tun 2007.