Real Madrid da Man City sun tashi 1-1 a Champions League

Chamiopns League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid da Manchester City sun tashi 1-1 a wasan farko a daf da karshe a Champions League ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Vinicius Junior a minti na 36 da fara wasa, yayin da City ta farke ta hannun Kevin de Bruyne a minti na 67.

Ranar Laraba 17 ga watan Mayu, City za ta karbi bakuncin Real a wasa na biyu a daf da karshe a babbar gasar zakarun Turai a Etihad.

A kakar bara Real Madrid ta fitar da City a daf da karshe da cin 6-5 gida da waje, bayan da kungiyar Sifaniya ta fara rashin nasara 4-3 a Etihad, amma ta ci 3-1 a Santiago Bernabeu a karawa ta biyu.

Real Madrid da Manchester City sun kece raini sau tara kenan a Champions League, kowacce ta ci karawa uku-uku da canjaras uku.

Sun fara wasa a tsakaninsu ranar Talata 12 ga watan Satumbar 2012, inda Real ta yi nasarar cin 3-2.

Wasa tsakanin Real Madrid da Manchester City:

Champions League Talata 9 ga watan Mayun 2023

  • Real Madrid 1 - 1 Man City

Champions League Laraba 4 ga watan Mayun 2022

  • Real Madrid 3 - 1 Man City

Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2022

  • Man City 4 - 3 Real Madrid

Champions League Juma'a 7 ga watan Agustan 2020

  • Man City 2 - 1 Real Madrid

Champions League Laraba 26 ga watan Fabrairun 2020

  • Real Madrid 1 - 2 Man City

Champions League Laraba 4 ga watan Mayun 2016

  • Real Madrid 1 - 0 Man City

Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2016

  • Man City 0 - 0 Real Madrid

Champions League Laraba 21 ga watan Nuwambar 2012

  • Man City 1 - 1 Real Madrid

Champions League Talata 18 ga watan Satumbar 2012

  • Real Madrid 3 - 2 Man City