Mario Balotelli ya koma taka leda a Serie A

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon ɗan wasan Manchester City da Liverpool da Ac Milan, Mario Balotelli ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Genoa na Seria A kan cinikin kyauta.

Ɗan wasan mai shekaru 34 ya kasance ba shi da kulob tun lokacin da ya bar ƙungiyar Adana Demirspor ta Turkiyya a bazara.

Balotelli, wanda ya buga wa Italiya wasa 36, ​​ya koma taka leda a ƙasarsa fiye da shekaru uku bayan ya bar Monza.

Ɗan wasan na cikin tawagar Manchester City da ta lashe gasar Firmiyar Ingila a shekarar 2012, ya koma ƙungiyar Genoa da halin yanzu ke fama ƙalubale a serie A ta bana.

Genoa, ƙarƙashin jagorancin Alberto Gilardino, tana matsayi na 18 bayan da ta samu maki shida a wasanni tara na farko.

Balotelli ya zura kwallaye 30 a cikin shekaru biyu da rabi tare da Manchester City, inda ya taimaka wa ƙungiyar ta lashe gasarta ta farko tun shekarar 1968.

Bayan ɗan gajeren lokaci a AC Milan, ya koma Liverpool inda ya kasa samun tagomashi a 2014, wanda ya haifar komawarsa San Siro a matsayin aro.

Tun daga wannan lokacin Balotelli ya buga wasanni a faɗin Turai a ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da Nice da Marseille na Faransa da Brescia da Monza na Italiya.