Trump ya lafta wa ƙasashe sabon haraji

Fadar gwamnatin Amurka ta sanar da sababbin harajin da ta sanya wa gomman kasashe da ke shigar da hajojinsu kasarta – wadanda ba su kai ga cimma yarjejeniyar kasuwanci da ita ba zuwa yanzu.
Yawanci harajin zai fara aiki ne a kwana bakwai masu zuwa, wanda hakan ya bayar da kofar cimma matsaya a tsakaninsu.
Kanada na daga cikin kasashen da Amurkar ta fi lafta wa harajin inda Shugaba Trump ya kara mata daga kashi 25 cikin dari zuwa kashi 35, wasu kasashen ma ya kai har kashi 41.
Wannan ce ranar da ya kamata ta kasance wadda harajin da Shugaba Trump na Amurkan ya ayyana a matsayin na Ranar 'Yanci ya kamata ya fara aiki.
A maimakon hakan sai fadar gwamtain kasar ta sanar da wasu jerin sababbin haraje-harajen ga kasashen da ke kasuwanci da ita – inda ya ci gaba da dambarwar kasuwanci da ya kulla da kasashen duniya.
Karin harajin ya kai har kashi hamsin cikin dari ga wasu kayayyakin da ake shigarwa Amurkar.
Zuwa yanzu dai Trump din ya sanar da yarjeniyoyi takwas, ciki har da wadda ya kulla da Tarayyar Turai da Japan da Birtaniya, kodayake har yanzu babu wani cikakken bayani game da dukkanin wadannan yarjeniyoyi da ya cimma da su.
Kasashe kadan ne suka tsira daga harajin nasa zuwa yanzu.
Kayayyakin da ake shigarwa daga makwabciyar Amurkar Kanada su ya fi lafta wa haraji inda ya kara daga kashi 25 cikin dari zuwa kashi 35 cikin dari.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun da farko kuma Amurkar ta bai wa wata makwabciyar tata – Mexico karin kwana casa'in ta hanzarta ta cimma yarjejeniya da ita.
Thailand, wadda a da take fuskantar harajin kashi 36 cikin dari a yanzu ta samu ragi zuwa kashi 19 cikin dari, kamar yadda sauran kasashe a yankinta suma suka ci moriyar hakan – kasashe irin su Indonesia da Philippines.
Taiwan ma na fuskantar harajin kashi 20 cikin dari , to amma ba a sani ba ko masana'antarta ta kera kayayyakin kwamfuta za ta samu harajinta na daban ne daga Amurkar.
India ta samu nata kason na harajin Trump din na kashi 25 cikin dari a hajojinta da take shigarwa Amurka, yayin da ya lafta wa Afirka ta Kudu kashi 30 cikin dari.
Dukkanin wannan harajin dai kamfanonin kasashen da ke shigar da hajojinsu Amurkar ne za su rinka biya.
Masana dai sun yi gargadin cewa karshenta masu sayen kayayyakin ne za su dandana kudarsu da sayen kayan da tsada a sanadiyyar harajin, da kuma haddasa tashin farashin kayayyaki.










