Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kocin Inter Miami bai san da tafiyar Messi Barcelona aro ba, Giroud ya zama golan Genoa
Kocin Inter Miami Tata Martino ya ce bai san komai ba game da raɗe-radin da ake yi na cewa Lionel Messi, zai tafi Barcelona aro a lokacin da aka kammala gasar Amurka, daga ƙarshen watan nan na Oktoba zuwa Fabarairu. (Goal)
AC Milan ta sanya ɗan wasan gaba na Faransa Olivier Giroud a cikin jerin sunayen masu tsaron ragarta, bayan ya yi nasarar ceton ƙungiyar daga ci a daidai lokacin tashi a wasan ranar Asabar da suka yi nasara a kan Genoa.
Ɗan wasan mai shekara 37 ya maye gurbin golan ƙungiyar ne Mike Maignan, wanda alƙalin wasa ya ba jan kati a minti na 97 a wasan. (FourFourTwo)
Wayne Rooney, na kan hanyar zama kocin ƙungiyar Birmingham City ta gasar ƙasa da Firimiya (Championship) , bayan da ya ajiye aikin horad da ƙungiyar DC United ta Amurka. (Times)
Rooney zai ɗauki tsohon abokin wasansa a tawagar Ingila Ashley Cole da kuma abokin wasansa a Manchester United John O'Shea zuwa Birmingham City idan har ƙungiyar ta yanke shawarar maye gurbin kocinta na yanzu John Eustace. (Mirror)
Ajax za ta tattauna makomar kocinta Maurice Steijn bayan da ƙungiyar ta faɗa cikin ƙungiyoyi uku na ƙasa a babbar gasar Holland bayan rashin nasara na uku da ta yi a jere. (Fabrizio Romano)
Tsohon kocin Ajax Louis van Gaal, wanda a kwanan nan ya zama mamba a cikin kwamitin masu lura da ƙungiyar ya halarci wasan da ta yi rashin nasara na baya-bayan nan 2-1 a gidan AZ Alkmaar ranar Lahadi. (Talksport)
Manchester United na sa ido tare da bin diddigin matashin ɗan wasan tsakiya na Palmeiras Luis Guilherme da kuma dan gaba na gefe na Flamengo Lorran, dukkanninsu masu shekara 17, amma kuma watakila sai ta kashe wajen fam miliyan 100 kafin ta samu ƴan Brazil ɗin biyu. (Star)
Sevilla na fatan gaggawar samun wanda zai mata koci bayan da ta kori Jose Luis Mendilibar a ranar Lahadi.
Kocin wanda ya taimaka wa ƙungiyar ta ɗauki kofin Europa na bakwai a kakar da ta gabata, ya yi nasara a wasa biyu ne kawai a cikin takwas a gasar La Liga ta bana. (AS)
Brentford na duba yuwuwar sayen matashin ɗan wasan gaba na gefe na Sunderland Jack Clarke ɗan Ingila a kan fam miliyan 15 a watan Janairu. (Alan Nixon via Chronicle)
Bajamushe Danny Rohl, mai shekara 34, wanda ya taɓa aikin kociya a RB Leipzig, da Bayern Munich da kuma tawagar Jamus, na dab da zama kocin Sheffield Wednesday. (Mail)
Tsohon ɗan wasa gaba na Chelsea, da Newcastle, da kuma Crystal Palace Loic Remy ya sanar da yin ritaya daga wasa, yana da shekara 36. Bafaranshen ya kasance ba shi da ƙungiya tun bayan da Brest ta bar shi da bazara. (Sun)