Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gaske ne ƴan arewacin Najeriya hukumar DSS ta kora daga aiki?
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kori wasu jami'anta 115 daga aiki sannan ta gargaɗi ƴan Najeriya da su kula yayin mu'amila da wasun su da ke ayyana kansu a matsayin jami'an hukumar.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, a ranar Talata, DSS ta shawarci al'umma su kauce wa mu'amala da jami'an a matsayin wakilan hukumar.
Hukumar ta kuma wallafa sunaye da hotonan jami'an 115 da ta ce ta kora a shafinta intanet.
'Ƴan Arewa ake kora'
Wani jami'in hukumar ta DSS wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa shi a fahimtarsa ana son a rage yawan jami'an hukumar ne ƴan asalin arewacin Najeriya.
"Ai tukunna ma. Ba ku ga komai ba. Za a yi babbar kora nan gaba. Wannan somin taɓi ne. Idan ka duba da kyau kusan wadanda aka kora ɗin za ka ga an ɗauke su aiki ne a shekaru bakwai da suka gabata wato lokacin jagorancin tsohon shugaban hukumar, Yusuf Magaji Bichi," in ji jami'in hukumar.
Ya ƙara da cewa tunda sabon shugaban hukumar ya kama aiki hankalinsu bai kwanta ba.
"Wallahi mu tunda ya fara aiki a watan Agustan 2024 hankalinmu ya fara tashi domin an faɗa mana cewa zai kori duk mutanen da tsohon DG ya ɗauka waɗanda kuma mafi yawanci ai daga arewa suke." Kamar yadda jami'in ya yi ƙarin haske.
"Gaskiya ba ƴan arewa ba ne kaɗai"
Shi ma wani jami'in hukumar wanda BBC ta sirranta sunansa ya shaida wa BBC cewa shi a fahimtarsa batun korar ƴan arewacin Najeriya bai taso ba.
"Gaskiya idan ka duba an kwashe shekaru bakwai da suka gabata ana ɗibar mutane aiki da yawa ciki har da waɗanda ma kwata-kwata ba su cancanci a ce su jami'an hukumar ba ne."
"To yanzu shi kuma sabon shugaban hukumar yana son ya samar da gyara ga hukumar ta fannin dawo mata da ƙimarta. Hakan ne ya sa duk wani wanda yake da wani tabo ko kuma aka ɗauke shi ba bisa cancanta ba da dai sauran su to su ne aka sallama bayan yin dogon bincike." In ji jami'in.
"Sannan idan ka kalli hotunan da sunayen mutanen za ka fahimci cewa waɗanda aka kora sun fito daga dukkan sassan Najeriya wato Kudu da Arewa. Ni na gane mutane suna son samun wani dalili su rinƙa yayata magana domin buƙatar kansu."
Ya ƙara da kwatanta abin da ya faru a hukumar da irin abin da ya faru a babban bankin Najeriya, CBN, inda bankin ya kori wasu ma'aikata masu yawa da sunan sauye-sauye da ake son a samar a babban bankin.
Abin da ya sa muka kori jami'ai 115 - DSS
Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kori mutanen ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.
Duk da cewa hukumar ta DSS ba ta fito fili ta faɗi laifukan da jami'an nata da ta kora suka aikata ba, amma a shafinta na X, ta ce ta ɗauki matakin korar ne bisa abin da ta kira wasu sauye-sauye da hukumar ke yi.
Sai dai kuma hukumar ta gargaɗi al'ummar ƙasar da su yi hankali da tsoffin jami'anta guda biyu Barry Donald da Victor Onyedikachi Godwin waɗanda ta amma har yanzu suna ayyana kansu a matsayin jami'an DSS.
Matakin na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama tsoffin jami'an nata biyu bisa zargin amfani da sunan hukumar suna damfarar mutane.
BBC ta kira lambar mai magana da yawun hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya dangane da jin dalilin sallamar ma'aikatan amma bai ɗauki kiran ba.
Kafar ta kuma aike wa mai magana da yawun hukumar saƙon Whatsapp dangane da zarge-zargen da wasu ƴan arewacin ƙasar suke yi cewa sallamar jami'an wani shiri ne na kakkaɓe ƴan arewaci daga hukumar, amma bai mayar da martani ba.
Da zarar kakakin hukumar ya mayar da martani, za mu sanya shi a wannan muƙalar.
Wane shugaban hukumar DSS?
A ranar 26 ga watan Agustan 2024 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin Mista Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin shugaban hukumar ta DSS.
Mista Ajayi wanda ya fara aiki a hukumar DSS a shekarar 1990, ya riƙe hedikwatar hukumar a jihohin Rivers da Bayelsa da Bauchi da Enugu da Kogi.
Adeola Ajayi ya karɓi jagorancin hukumar daga hannun Yusuf Magaji Bichi, tsohon shugaban hukumar wanda ya jagorance daga watan Satumbar 2018 zuwa Agustan 2024.
A 2018 ne shugaba Muhammadu Buhari ya nada Bichi a matsayin shugaban hukumar ta jami'an farin kaya ta DSS, bayan da aka sauke Lawal Musa Daura daga jagorancin hukumar a watan Agustan 2018.