Ku San Malamanku tare da Sheikh Sabo Ibrahim Sani
Ku San Malamanku tare da Sheikh Sabo Ibrahim Sani
An wallafa
A wannan makon za mu kawo shugaban makarantar Sabilarrashad a jihar Nasarawa, Sheikh Sabo Ibrahim Sani.
Sheikh Sabo ya ce tun yana yaro yake koyar da mutanen da suka girme shi da waɗanda suke sa'anninsa.
Dangane da abin da ya shafi fannin karatun zamani, ya kwashe shekaru 29 wajen neman takardun shedar kammala firamare da sakandire da difiloma da digiri na ɗaya da na biyu da na uku a ɓangaren harshen Larabci.
Sai dai Sheikh ya ce kafin nan sai da ya yi karatun Qur'ani a tsangaya da kuma karatun littafai a gaban malamai.



