Yadda taron Ecowas ya gudana a Abuja
Yadda taron Ecowas ya gudana a Abuja
An wallafa
A ranar Alhamis ne shugabannin kungiyar Ecowas ta gudanar da taron gaggawa a Abuja babban birnin Najeriya domin dauykar mataki kan sojojin da suka gudanar da juyin mulki a Nijar.
Shugabannin ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.
Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen




