Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta bai wa Real tazarar maki 9 bayan cin Espanyol
Barcelona ta doke Espanyol 3-1 a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi karawar mako na 12.
Barcelona ta fara cin ƙwallo ta hannun Dani Olmo a minti na 12 da fara wasan, sannan shi ne ya kara na biyu a minti na 19 tsakani daga nan Raphinha ya zura na uku a raga kan hutu.
Espanyol ta zare ɗaya ta hannun Javi Puado a zagaye na biyu.
Da wannan sakamakon Barcelona, wadda ta buga karawa 12 ta ci gaba da zama a matakin farko a kan teburi da maki 33 da tazarar tara tsakani da Real Madrid mai 24.
Real Madrid ba ta buga wasa ba da Valencia a makon nan, sakamkon ambaliyar ruwa da abin ya fi muni a wasu sassan Sifaniya.
Ranar Laraba Barcelona za ta je Red Stars, domin buga Champions League daga nan Real Sociedad ta karɓi bakuncin Barcelona a La Liga ranar 10 ga watan Nuwamba.