Atletico ta cimma yarjejeniyar ɗaukar Le Normand daga Real Sociedad

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Ƙwallon kafa ta Atletico Madrid ta cimma yarjejeniya kan ɗaukar ɗan wasan tawagar Sipaniya, Robin le Normand daga Real Sociedad.
Ɗan wasan mai shekaru 27 ya taimakawa kasarsa lashe gasar cin kofin nahiyar Turai, Euro 2024, wadda aka kammala a Jamus cikin watan Yuli.
Atletico ta ce "Nan da ƴan kwanaki za a kammala cinikin ɗan wasan, lokacin da ya kammala hutu".
Real Sociedad ta tabbatar da ƙulla yarjejeniya da abokiyar hamayyar ta a La Liga, wato Atletico kan sayar da ɗan wasan da ya taimaka mata lashe Copa del Rey a shekarar 2021.
"Robin ya je birnin Zubieta a shekarar 2016, bayan shekara biyu tare da Sanse, ya fara buga wasa a kaka ta uku da shiga cikin ƴan 11 farko," in ji Real Sociedad.
"Ya ci gaba da taka rawar gani a ƙungiyar da yin fice, wanda ya buga wasa 221 da ɗaukar Copa del Rey.







