Muhimman sauye-sauye shida da za a yi wa tsarin zaɓen Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce ta yi nazari tare da samar da wasu shawarwari kan yadda za a yi wa harkar zaɓen ƙasar garanbawul domin inganta shi kafin ƙarshen shekarar 2025, don shirya wa zaɓuka na gaba.

Hukumar ta ce buƙatar yin gyaran ta taso ne daga shawarwarin da ta samu daga masu ruwa da tsaki da suka yi nazari game da yadda aka gudanar da babban zaɓen 2023.

Inec ta ce daga ckin shawarwarin da ta tattara akwai waɗanda ke buƙatar ɗaukar matakin gyara daga ita kanta hukumar da waɗanda suka shafi sauran masu ruwa da tsaki irin su jami'an tsaro da kamfanonin sadarwa da jam'iyyun siyasa da kuma hukumomin tabbatar da ingancin aiki.

Sauran ɓangarorin da buƙatar gyaran ta shafa sun haɗa da ƙungiyoyin masu aikin sufuri da ƙungiyoyin fararen hula da kuma kafafen yaɗa labarai.

Saboda da haka hukumar ta ce za ta gabatar da wani cikakken rahoto mai neman tabbatar da wannan ƙudiri na yin garamabawul ga tsarin zaɓen Najeriya, ga kwamitocin majalisar dokokin tarayya domin su yi aiki a kai da kuma tabbatar da su.

Inec ta gabatar da wannan buƙata ne a ƙarshen babban taronta na ƙasa, wanda shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya jagoranta a ranar Alhamis, 12 ga watan Dismaba.

BBC ta tattauna da jami'ar hulɗa da jam'a ta hukumar Inec, Zainab Aminu, domin samun ƙarin haske kan sabbin sauye-sauyen.

Yin zaɓe ba tare da katin zaɓe na dindindin ba

Hukumar INEC na neman a bayar da damar kaɗa ƙuri'a ga mutanen da ba su mallaki katin zaɓe na dindindin ba, in dai an yi masu rijista.

Hakan na nufin "hukumar zaɓe tana duba yanayin da idan mutum ya je da katin zaɓe na wucin-gadi, ko kuma ya je rumfar zaɓe ya gabatar da lambobin da ke jikin katin nasa, za a iya tantance shi domin kaɗa ƙuri'a,'' in ji Zainab Aminu.

Wannan zai tabbata ne ta amfani da sabuwar na'urar tantance masu zaɓe ta Bimodal Voter Accreditation System, wadda ta ke ɗauke da bayanan dukkan masu zaɓe da aka yi wa rajista.

Hukumar na ganin cewa wannan tsari zai taimaka wajen rage sayar da ƙuri'a a lokacin zaɓe.

A yanzu dai dole ne sai wanda ke da katin zaɓe na dindindin ne zai iya kaɗa ƙuri'a a Najeriya, bayan ya gabatar da katin nasa a rumfar zaɓe.

Kaɗa ƙuri'a kafin ranar zaɓe

INEC tana kuma neman a yi sabon tsari da zai bayar da dama ga mutane da ke yin ayyuka na musamman domin su kaɗa ƙuri'a kafin ranar zaɓen gama-gari.

''Hukumar zaɓe tana neman a bayar da damar yin abin da ake kira 'early voting' ta yadda ƴan jarida da ma'aikatan zaɓe da jami'an tsaro da dai duk waɗanda ke yin aiki a ranar zaɓe,'' kamar yadda jami'ar ta yi wa BBC bayani.

Wannan zai kawar da matsalar da ake fuskanta a tsarin da ake kai yanzu, ta yadda masu aiki na musamman ba za su samu damar yin zaɓe ba saboda yanayin aikin nasu.

Akwai ƙasashe da dama waɗanda ke amfani da irin wannan tsari kasancewar sau da dama masu ayyuka na musamman kan rasa damarsu ta kaɗa ƙuri'a sanadiyyar ayyukan da suke yi a ranar zaɓe.

Zaɓe daga ƙasashen waje

Wani batun da Inec ɗin ke ƙoƙarin ganin ya samu shiga tsarin zaɓen Najeriya shi ne zaɓe daga ƙasashen ƙetare.

Wannan wani tsari ne da zai bai wa ƴan Najeriya mazauna wasu ƙasashen duniya damar kaɗa ƙuria duk da cewa ba sa gida.

A halin yanzu duk wani ɗan Najeriya da ke rayuwa a wata ƙasa ta daban ba ya da damar kaɗa ƙuri'a sai dai idan ya koma gida.

Sai dai idan ana son tabbatar da wannan tsari sai an samar da abubuwan da za su bayar da damar tantancewa da kaɗa ƙuri'ar daga waje.

Tsaftace rajistar zaɓe

INEC ta kuma yi aniyar sabunta rajistar zaɓe domin tsaftace ta don ɗaukar bayanan haƙiƙanin mutanen da suka yi rajista kuma suke rayuwa a daidai lokacin da ake shirin amfani da rijisatar.

Domin cimma nasarar hakan, hukumar zaɓen ta Najeriya ta ce za ta yi aikin haɗin gwiwa da hukumar rajistar ƴan ƙasa ta Najeriya wato, National Identity Management Commission da kuma hukumar ƙidaya ta Najeriya.

Dama akwai masana da ke ganin cewa za a iya haɗa rajistar zaɓen Najeriya da sauran muhimman takardu kamar na rajistar ƴan ƙasa domin samun sauƙin gudanarwa.

Inganta tsarin sufuri

Hukumar zaɓen ta Najeriya tana kuma duba yadda za ta inganta tsarin jigilar ma'aikata da sauran kayan aikin zaɓe zuwa sassan ƙasar a lokacin zaɓuka na gaba.

Wannan na daga cikin ɓangarorin da masu sharhi suka daɗe suna kiran a yi gyara domin tafiya daidai da zamani da kuma kaucewa kura-kuren baya.

Malama Zainab Aminu ta ce ''INEC tana sane da irin waɗannan matsaloli kuma ta yarda cewa ya kamata a ɗauki matakan magance su''.

Tura sakamakon zaɓe ta intanet

Haka nan kuma INEC ta ƙoƙari domin samun hukuncin kotu a game da yadda ake aikawa da sakamakon zaɓe daga rumfuna zuwa babbar cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta intanet.

A wannan ɓangaren hukumar tana neman kotu ta yanke hukunci kan dambarwa game da ingancin tura sakamakon zaɓe ta intanet ko kuma aikawa da shi hannu da hannu.