Barcelona za ta sake daukar dan bayan Arsenal Hector Bellerin

An wallafa

Dan wasan bayan Spaniya Hector Bellerin zai sake komawa Barcelona bayan karewar kwantaraginsa a Arsenal.

Yarjejeniyar za ta hada da biyan wasu kudi ga duk kungiyar da za ta dauki dan wasan idan zai bar Nou Camp.

Dan wasan ya koma Arsenal ne daga Barcelona a 2011, ya kuma buga wasa a kakar da ta kare a Real Betis a matsayin aro.

Dan wasan mai shekara 27 ya buga wa Arsenal wasan share fagen shiga kakar wasanni, amma bai buga mata ko wasa guda ba a wasannin Premier da ta yi.

Bellerin ya buga wa Arsenal wasa 239 a zamansa a kungiyar ta Landan.

A gefe guda kuma dan wasan da yake buga gefen dama a Barcelona Sergino Dest yana AC Milan ana duba lafiyarsa zai koma kungiyar a matsayin aro.

Dan wasan kasar Amurkan Dest mai shekara 21 ya koma Barcelona ne a 2020 daga Ajax ya kuma bugawa kungiyar wasa 73.