Chelsea ta doke Man City a kan Cucurella

An wallafa

Chelsea ta sayi dan bayan Sifaniya Marc Cucurella daga kungiyar Brighton tsawon shekara shida.

Matashin dan bayan na gefen hagu mai shekara 24 ya ci kwallo daya kacal a wasa 38 da ya yi a kaka daya kawai da ya yi wa Brighton bayan da suka saye shi daga Getafe.

Brighton ta nemi Fam miliyan 50 ne a kan dan wasan wanda Zakarun Premier Manchester City suka nema domin maye gurbin Oleksandr Zinchenko wanda ya koma Arsenal.

Sai dai kungiyar ta Pep Guardiola ta taya shi Fam miliyan 30 abin da kungiyar tasa ta ki.

Bayanin cinikin na nuna cewa Chelsea ta saye shi a kan sama da Fam miliyan 60.

Dan wasan ya bayyana irin farin cikin da yake cikin bayan kammala cinikin.

Ya ce, ''Ina matukar farin ciki. Babbar dama ce gare ni shiga daya daga cikin manyan kungiyoyi na duniya."

"Zan yi aiki tukuru don na samu farin ciki a nan na kuma taimaka wa kungiyar." in ji shi.