Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Barcelona za ta koma ta daya a La Liga ranar Asabar?
Barcelona za ta karbi bakuncin Almeria a wasan mako na 13 a gasar La Liga ranar Asabar a Nou Camp.
Idan an kammala karawar mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya za a yi hutu har sai bayan an kare gasar cin kofin duniya a Qatar.
Wannan karawar ita ce ta karshe da Gerrard Pigue zai yi wa Barcelona, wanda ranar Alhamis ya sanar da zai yi ritaya, wanda ya lashe kofi kimanin 30.
Almeria ta koma buga La Liga a bana, bayan shekara bakwai rabon ta da babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ta fara kakar bana da kalubale, amma yanzu ta bar gurbin 'yan kasan teburi ta yi sama kadan da cin wasa uku a gida, sai dai ba ta kokari a karawar waje.
Cikin wasa 14 da kungiyoyin suka kara a tsakaninsu a lik da kofuna, Barcelona ba ta taba rashin nasara a hannun Almeria ba.
Haka kuma kungiyar Nou Camp kan lashe dukkan karawar da ta yi da Almeria a gida a dukkan fafatawar da suka yi.
Barcelona za ta buga wasan a mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki daya tsakani da Real Madrid.
Idan Barcelona ta ci wasan za ta koma ta daya na kwana biyu kafin sakamakon karawar Real Madrid da Rayo Vallecano na hanayya ranar Litinin.
Za a fara gasar kofin duniya ranar 20 ga watan Nuwamba a karkare ranar 18 ga watan Disambar 2022.