Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla
Real Madrid ta lashe La Liga na kakar nan na 36 jimilla, bayan da Barcelona ta yi rashin nasara 4-2 a gidan Girona ranar Asabar.
Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta doke Cadiz 3-0 a gasar mako na 34 da suka kara a Santiago Bernabeu.
Minti 45 din farko ba ci a tsakanin kungiyoyin, bayan da suka yi hutu suka koma karawar zagaye na biyu ne Real ta ci kwallayen uku.
Tun farko Brahim Diaz ya fara ci, sai Jude Bellingham ya kara na biyu da kuma Joselu da ya zura na uku a raga a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Mai tsaron raga, Thibaut Cortois ya buga wasan na ranar Asabar, kuma a karon farko a kakar nan, wanda ya yi jinyar wata tara.
Real Madrid, wadda ta buga wasa 34 ta lashe La Liga saura karawa hudu a kammala kakar bana ta lashe karawa 27 da canjaras shida aka doke ta wasa daya.
Haka kuma kungiyar Santiago Bernabeu ta ci kwallo 74 aka zura mata 22 a raga da maki 87.
Real ta samu damar lashe kofin bana, bayan da Girona ta doke Barcelona 4-2 a wasan hamayya ranar Asabar a Estadi Montilivi.
Hakan ya sa Girona ta koma ta biyu da maki 74, ita kuwa Barcelona mai maki 73 ta yi kasa zuwa ta ukun teburin La Liga.
Kenan Real ta bayar da tazarar maki 14, kuma saura wasa hudu suka rage kenan maki 12 a kasa, sakamakon ya nuna ba wadda za ta tarar da ita a yawan hada maki.
Da Barcelona ce ta yi nasara a kan Girona, kenan Real na bukatar samun maki daya nan gaba, amma tunda ita aka doke shi kenan Real ta dauki La Liga na bana na 36 jimilla.
Wannan shi ne La Liga na biyu da Ancelotti ya lashe a Real Madrid, bayan 2021/22.
Yanzu hankalin Real zai koma wasan da za ta karbi bakuncin Bayern Munich a karawa ta biyu ta daf da karshe a Champions League ranar Laraba.
Real Madrid mai Champions League 14 ta tashi 2-2 a wasan farko a gidan Bayern Munich mai shida a Allianz Arena ranar Talata.
Jerin ƴan wasan dake kan gaba a cin kwallaye:
- Artem Dovbyk Girona 20
- Jude Bellingham Real Madrid 18
- Robert Lewandowski Barcelona 17
- Alexander Sorloth Villarreal 17
- Ante Budimir Osasuna 16
- Borja Mayoral Getafe 15
- Alvaro Morata Atletico Madrid 14
- Antoine Griezmann Atletico Madrid 13
- Hugo Duro Valencia 13
- Vinicius Junior Real Madrid 13
- Gorka Guruzeta Athletic Bilbao 12
- Youssef En-Nesyri Sevilla 12
Jerin wadanda ke kan gaba a yawan lashe La Liga
- Real Madrid 36
- FC Barcelona 27
- Atletico de Madrid 11
- Athletic de Bilbao 8
- Valencia 6
- Real Sociedad 2
- Deportivo La Coruna 1
- Sevilla 1
- Real Betis 1