Masu takarar lashe takalmin zinare a Bundesliga

An wallafa

Ranar 30 ga watan Satumba za a ci gaba da wasannin mako na takwas a gasar Bundesliga, inda Union Berlin ce ke jan ragamar teburi.

Haka kuma dan wasanta Sheraldo Becker shi ne kan gaba a masu takarar lashe takalmin zinare a babbar gasar tamaula ta Jamus ta bana.

Sadio Mane da Christopher Nkunku suna daga cikin masu fatan lashe kyautar, idan an kammala kakar nan.

Tun cikin karni na 1960 zuwa 1970 dan kwallon Bayern Munich, Gerd Muller ya gagari kowa, wanda ya lashe kyauta takalmin zinare bakwai a tarihi.

Daga nan kuma Robert Lewandowski ya karbi ragama mai bakwai jumulla, daya a Borussia Dortmund da shida a Bayern Munich.

Kyaftin din tawagar Poland ya zura kwallo 41 a kaka guda wanda ya lashe kyautar bara da cin kwallo 35 a raga.

To sai dai kuma Lewandowski ya koma taka leda a Barcelona a kakar nan, hakan ne ya sa ya bar gurbin takarar wanda zai lashe takalmin zinare a Bundesliga a kakar nan.

Haka kuma a bana Erling Haaland wanda shima ya yi kaurin suna wajen yawan cin kwallaye ya koma buga Premier League a Manchester City a bana.

Kawo yanzu dan wasan Union Berling, Sheraldo Becker shi ne kan gaba mai shida a raga.

Wasannin mako na takwas a gasar Bundesliga

Juma’a 30 ga watan Satumba

  • Bayern Munich da Bayer Leverkusen

Asabar 1 ga watan Oktoba

  • VfL Wolfsburg da       
  • SC Fribourg da FSV Mainz
  • Eintracht Frankfurt da  Union Berlin 
  • 1. FC Koln da Borussia Dortmund      
  • RB Leipzig da  Bochum           
  • SV Werder Bremen da Borussia Monchengladbach 

Lahadi 2 ga watan Oktoba

  • Hertha BSC da  Hoffenheim   
  • FC Schalke da  Augsburg

10 farko da ke takarar lashe takalmin zinare a Bundesliga a bana:

  • Sheraldo Becker                    1. FC Union Berlin 6
  • Niclas Fullkrug.                      SV Werder Bremen 5
  • Daichi Kamada.                      Eintracht Frankfurt 4
  • Jamal Musiala.                       FC Bayern Munich 4
  • Christopher Nkunku.             RB Leipzig 4
  • Michael Gregoritsch.             SC Fribourg 3
  • Vincenzo Grifo.                       SC Fribourg 3
  • Jonas Hofmann                      Borussia Monchengladbach 3
  • Jordan Siebatcheu.                 Union Berlin 3
  • Lukas Nmecha.                       VfL Wolfsburg 3
  • Marius Bulter.                         FC Schalke 3
  • Sadio Mane.                           FC Bayern Munich 3
  • Kerem Demirbay.                   Bayer 04 Leverkusen 3
  • Marcus Thuram                      Borussia Monchengladbach 3
  • Karim Onisiwo                         FSV Mainz  3
  •