Barau FC ta damƙa wa Rabi'u Tata aikin kociyanta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barau FC ta damƙa wa Rabi'u Tata aikin horar da ita, mai buga gasar Nigerian National League (NNL).

Tun farko ya ja ragamar wasa biyu a matakin riƙon ƙwarya, bayan da ta dakatar da Salisu Yusuf.

Cikin wasa biyu da Tata ya ja ragama ya fara da yin nasara a kan Sokoto United da cin 1-0 a Kano ranar 11 ga watan Janairu karawar mako na biyar.

Okeke Ekechikwu ne ya ci wa Barau FC kwallon a minti na biyar da suka koma zagaye na biyu a fafatawar.

A wasa na biyu Tata ya je ya tashi 1-1 da Zamfara United a wasannin mako na shida a gasar mai daraja ra biyu ta Najeriya ranar 19 ga watan Janairu.

Osondu Jonathan ne ya ci wa Barau FC ƙwallon da ya sa ta tashi canjaras a karawar daga ita aka je hutu a wasannin na NNL na bana.

A mako biyu da suka gabata Barau FC ta dakatar da Yusuf, wanda ya fara aiki kafin fara kakar bana, wanda ya ja ragamar wasa huɗu a gasar ta NNL.

A cikin karawar ya yi canjaras biyu a gida aka doke Barau FC fafatawa biyu da ta yi a waje a gasar ta Najeriya.

Kawo yanzu Barau FC wadda take shiyya ta uku tana da maki shida a mataki na biyar a ƙungiya bakwai, Wikki Tourist ce ta farko mai maki 13 a rukunin.

Yanzu ana hutu a gasar ta NNL, sai cikin watan Fabrairu za a ci gaba da wasannin zagaye na biyu.