Kvaratskhelia ya sanar da yin ban kwana da Napoli

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Khvicha Kvaratskhelia ya sanar da yin ban kwana da Napoli a wani sako da ya saka a kafarsa ta sada zumunta ranar Alhamis.

Ana kuma cewar ɗan wasan tawagar Georgia zai koma taka leda a Paris St Germain ta Faransa.

Ranar Asabar kociya, Antoni Conte ya sanar cewar Kvaratskhelia ya nemi barin Napoli mai buga Serie A nan take.

Kvaratskhelia ya koma Napoli a 2022, shi ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Serie A a 2022/23.

Hakan ya biyo bayan rawar da ɗan ƙwallon ya taka da ta kai Napoli ta lashe kofin Serie A, na farko da ta ɗauka tun bayan shekara 33.

A kakar ce Kvaratskhelia ya ci ƙwallo 12 ya kuma bayar da 13 aka zura a raga daga karawa 34 da ya buga.

Ɗan wasan mai shekara 23 yana da sauran kunshin yarjejeniya da Napoli da ya kamata ta kare a karshen kakar 2027.