Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta sha da ƙyar a gidan Palace a Premier
Sau biyu ana fara cin Manchester City tana farkewa a Crystal Palace da ta kai sun tashi 2-1 a wasan Premier League ranar Asabar.
City, wadda ta kawo karshen kasa cin wasa daga karawar bakwai a jere ta doke Nottingham Forest a tsakiya mako, kenan an sa ran za ta yi abin kirki a Selhurst Park.
Ƙungiyar da Oliver Glasner ke jan ragama ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Daniel Munoz, saura minti 15 su je hutu Erling Haaland ya farke na 13 da ya zura a raga a bana.
Ɗan wasan Norway ya yi kan-kan-kan da Mohamed Salah na Liverpool a jerin waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a Premier League a kakar nan.
Bayan da wasa ya kara yin nisa, sai Palace ta kara na biyu ta hannun mai tsaron baya, Maxence Lacroix, daga baya Rico Lewis ya farke.
Saura minti shida a tashi daga karawar aka bai wa Lewis jan kati, bayan katin gargadi da ya karɓa a karo na biyu, sakamakon ketar da ya yi wa Trevoh Chalobah.
Da wannan sakamakon City tana da tazarar maki takwas tsakaninta da Liverpool mai jan ragamar teburi, wadda aka soke wasan da ya kamata ta yi a Everton ranar Asabar, sakamakon makekiyar guguwa.
Ita kuwa Palace ta yi saman teburi da tazarar maki huɗu tsakaninta da ƴan ukun teburin Premier, bayan karawar mako na 15..