Kano Pillars za ta buga ƙwantan wasa da El-Kanemi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kano Pillars za ta kara da El-Kanemi Warriors a ƙwantan wasan mako na 20 ranar Laraba a gasar Premier ta Najeriya.

Ƙungiyar da ake kira sai masu gida za ta karɓi bakuncin El-Kanemi Warriors a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata a jihar Kano, Najeriya.

Ranar 29 ga watan Disambar 2024, El-Kanemi ta yi nasara a kan Pillars da cin 1-0 a wasan mako na 19.

El-Kanemi tana ta shidan teburi da maki 35, Pillars kuwa mai maki 29 tana ta 14 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Najeriya ta kakar nan.

Pillars za ta buga wasan karkashin kocin riƙon ƙwarya, Ahmad Yaro-Yaro sakamakon da aka dakatar da Usman Abdallah mako uku daga 2 ga watan Fabrairu.

A wata sanarwa daga jami'in ƴaɗa labaran ƙungiyar Ismail Abba Tangalash ta ce kociyan ya nuna halin rashin da'a, bayan tashi ba ci a wasa da Bayelsa ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano.

Haka kuma a ranar ta Laraba za a buga wasu ƙwantan wasan da ya haɗa da na Bendel Insurance da Enyimba da na Kwara United da Shooting Stars Sports Club (3SC).

Remo Stars ce ta ɗaya a kan teburi da maki 48, bayan wasan mako na 23, sai Shooting Stars Sports Club ta biyu da maki 40 da kuma Rivers United ta uku da maki 38.