Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba zan samu irin lokacin da Arteta ya samu a Arsenal ba - Amorim
Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya ce kulob ɗin ba zai ba shi isasshen lokacin da aka bai wa takwaransa, Mikel Arteta wajen samar da sauyi a Arsenal.
Arteta wanda ɗan ƙasar Sipaniya ne ya gaji Unai Emery a matsayin kocin Arsenal a watan Disamban 2019 inda ya taimaka wa kulob ɗin wajen riƙe kambu na tsawon lokaci.
Arteta ya samu nasarar lashe gasar kofin FA na 2020 a kakar farko ta wasanni sai dai kuma wannan ce kawai nasarar da ya samu tun bayan naɗin nasa - ya kwashe kaka uku kafin ya iya mayar da kulob ɗin komawa gasar Champions League.
"Ba zan samu lokacin da Arteta ya samu ba," in ji Amorim.
Sai dai kuma Amorim ya ce zai ɗauki darasi daga yadda Arteta ya iya shawo kan wasu matsaloli a farkon zuwansa Arsenal.
"Ina tunanin cewa [Arsenal] kulob ne da ya banbanta da sauran," Amorim ya ci gaba da faɗi.
"Kulob ne na daban, ta wannan fuskar, yadda Arteta ya iya warware matsaloli abu ne da kowa zai iya ɗaukar darasi."